magana Jari Ce 2 Audio

4.8 (36)

ترفيه | 73.2MB

تفاصيل التطبيق

Duba manhajjar nan ta hanyar amfani da wadannan kalmomi dake biye:
✔️ littafin magana jarice
✔️ magana jarice 2 audio
✔️ magana jarice 2 mp3
✔️ magana jarice audio
✔️ magana jarice littafi na biyu
✔️ magana jarice mp3
✔️ magana jarice na biyu
Saurari littafin magana Jarice littafi na biyu. Magana Jari ce littafi na biyu wallafar Alhaji Dr. Abubakar Imam kamfanin Gaskiya Zaria.
Wannan littafi, `Magana Jari ce, 2', yana cikin littattafai guda uku da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a cikin wata shida na zamansa a Zariya a shekarar 1936. Dalilin za6o shi kuwa ya rubuta wadannan littattafai shi ne ya shiga wata gasa to rubutun littafi a shekarar 1933 ya kuma ci nasara da littafinsa na farko 'Ruwan Bagaja'.
MAGANA JARICE LITTAFI NA BIYU - Yaro Bada Kudi A Gaya Maka!
A cikin magana jarice 2 akwai cikakkun labaru kamar haka:
☆ Magana Jari Ce
☆ Yaro Tsaya Matsayinka Kada Zancen 'Yan Duniya Ya Rudeka
☆ Baruan Arziki Da Mugun Gashi
☆ Kalala Da Kalalatu
☆ Yusha'u Na-Narimi Dutse Baka Fargaba
☆ Mara Gaskiya Ko Cikin Ruwa Yayi Jibi
☆ Ba Gaskiya Bace Abar Bida Ga Shariah, Kai Dai A Samo Sa'a
☆ Sarkin Noma Da 'Yayansa
☆ Da Muguwar Rawa Gwamma Kin Tashi
☆ Jimrau Dan sarkin Noma Na Biyu
☆ Labarin Wani Makaho
☆ Kosau Dan Sarkin Noma Na Fari
☆ An Ki Cin Biri An Ci Dila
☆ Gamuwar Kosau Da Jimrau Da Nomau
☆ Jarrabawar Da Aka Yiwa Sarkin Barayi Nomau
☆ Wadansu Madinka Su Uku
☆ Kuda Wajen Kwadayi Akan Mutu
☆ Yaro Bari Murna Karenka Ya Kama Zaki
☆ Kukan Kurciya Ma Jawabi Ne, Mai Hankali Ke Ganewa
☆ Labarin Wani Sarki Da yaronsa
☆ Zafin Nema Baya Kawo Samu
☆ Allah Na Taimakon Wanda Ya Taimaki Kansa
☆ Ja'iru 'Dan Sama Jannati
☆ Wadansu 'Yan Kama Da 'Yan Sama Jannati
☆ Sarkin Farisa Da Wani Bahindi
☆ Labarin Wadansu Samari Su Uku
☆ Kama Da Wane Ba Wane Ba Ne
☆ Labarin Sarki Kamaruzzaman Dan Sarki Shahruzzaman
☆ Amjadu Da Asadu
☆ Kyale Maketaci Yayi Ta Halinsa, Kome Ta Jima Zamani Na Nan
☆ In Maye Nada Hankali Baya Fid Da Maitarsa A Fili
☆ Iya Gani Iya Kyalewa
☆ Rana Ta karshe
An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin garin kagara sa'an nan tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya Yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil to Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta `Ruwan Bagaja'. Ganin kwazonsa wajen Raga labari mai ma'ana ya sa Dr. R.M. East shugaban Offishin Talifi na Zariya ya roki a ba da shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce rubuce a Zariya. Bayan ya koma Katsina aka bi shi da rokon ya kara rubuta wasu , littattafan. A can ya rubuta 'Karamin Sani kukumi' cikin 1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ya roka a dawo da Imam Zariya a koya mashi aikin edita ya zama editan jaridar farko to Arewa. Shi ne ma ya rada mata suna `Gaskiya Ta Fi Kwabo' aka fara bugawa a watan Janairu na shekara 1939.
Ya yi shekara 12 yana wannan aiki na edita har ma ya rubuta wani littafi a lokacin `Yakin Duniya Na Biyu' watau `Yakin Hitila' da ya ba suna `Tafiya Mabudin Ilmi'. Wannan littafi ya ba da Iabarin tafiyarsa tare da wasu editoci na jaridun Africa to Yamma zuwa Ingila a jirgin ruwa a shekara 1943.
Idan kunji dadin wannan manhajja ta magana jarice 2, sai ku ba manhajjar tauraro biyar, ku rubuta tsokacinku kuma sannan ku aikata zuwa ga yanuwa da abokai.

Show More Less

المعلومات

تحديث:

الإصدار: 1.0

نظام الأندرويد المتوافق: Android 4.1 or later

التقييم

مشاركة

ما قد تحب